1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Mozambique ya fara ziyarar aiki a Vietnam

January 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuUI

Shugaban kasar Mozambique, Armando Gebuza yau ne ya isa birnin Hanoi, domin fara ziyarar aiki na tsawon kwanaki biyar a Vietnam.

Mr Gebuza dai zai gudanar da shawarwari da takwaran aikin sa na Vietnam, Nguysen Minh Triet da shugaban majalisar dokokin kasar da janar sakatare na jam’iyar kwaminis.

Ana sa ran shugaban na Mozambique zai sanya hannu kann yarjeniyoyin da suka shafi hadin kai tsakanin kasashen biyu a fannonin ilimi da al’adu da kiwon lafiya da aiyukan noma.

A Lokacin ziyarar tasa, Mr Gebuza zai kuma shugabanci taron kwamitin tattalin arziki na hadin gwiwa tsakanin Vietnam da Mozambique, kafin ya zarce zuwa birnin Ho Chi Minh, inda zai yi tattaki na kwanaki biyu domin gabnawa da yan kasuwa da masu masana’antu.