1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaba Buhari ya amince da kasafin 2016

Ubale Musa/YBMay 6, 2016

Akalla Naira miliyan dubu 200 ne dai gwamnatin kasar ta ware don sake ginin hanyoyi, a cikin kasafin da zai lamushe Naira tiriliyan daya da miliyan dubu 760 domin manya na aiyyuka.

https://p.dw.com/p/1IjK9
Niger Buhari Issoufou
Shugaba Muhammadu Buhari na NajeriyaHoto: DW/M. Kanta

An dai dauki tsawon lokaci ana kai kawo kuma har an kai ga korafin rashi na gaskiya, to sai dai kuma an kare tare da shugaban Najeriyar Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan kasafin kudin kasar na shekarar bana na Naira tirilliyan shida da milliyan dubu sittin.

Kasafin dai na zama na farko na sabuwar gwamnatin kasar, kuma zakaran gwajin dafi ga tasirinta a tsakanin al'umma.

Ana dai kallon share watanni har guda biyar ana zaman jiran ganin kokari na aiwatar da kasafin da ma tasirinsa tsakanin al'umma.

Nigeria Bukola Saraki
Bukola Saraki shugaban majalisar dattawaHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

To sai dai kuma a fadar karamar ministar tsarin kasafin Hajiya Zainab Shamsuna mahukuntan na Abuja sun shirya tsaf da nufin cika buri na 'yan kasar tare da tanadi na duk kudaden da ake da bukata yanzu.

Babban kalubale da ke gaban kasafin da ke zaman mafi girma a cikin tarihi na kasar dai na zaman kashe tsabar kudi har tiriliyan shida da doriya cikin watanni kasa da bakwai ba tare da fuskantar matsala ba, ko dai ta karfi na hukumomi na gwamnatin ko kuma cin hancin da ya gurgunta 'yan uwansa a baya.

Kokarin cusa na goron a bangaren 'yan dokar ne dai ya kai ga jan kafa da ma ka-ce-na-cen da ta mamaye aikin kasafin can baya.

Matsin lamba don aiwatar da kasafin

To sai dai kuma a fadar Yakubu Dogara da ke zaman shugaban majalisar wakilai ta kasar, 'yan dokar ba su da niyya ta sarara wa bangaren zartarwar wajen aiwatar da kasafin kamar yadda aka tsara.

Nigeria Kabinett Muhammadu Buhari Präsident
Zauran majalisar zartarwa a NajeriyaHoto: Reuters/A.Sotunde

Tuni dai gwamnatin kasar ta ce ta kafa wani kwamiti da nufin fara aikin kasafin kudin kasar a shekarar da ke tafe, da nufin kauce wa rigingimu shigen wadanda kasafin na bana ya fuskanta.

Akalla Naira miliyan dubu 200 ne dai gwamnatin kasar ta ware don sake ginin hanyoyi, a cikin kasafin da zai lamushe naira triliyan daya da miliyan dubu 760 domin manya na aiyyuka, sannan kuma da naira tiriliyan biyu da miliyan dubu 347 domin harkokin yau da na gobe.