1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Najeriya zai kai ziyara Kamaru

Salissou BoukariJuly 28, 2015

Shugaban Tarayyar Najeriya Muhammadu Buhari zai kai ziyara a kasar Kamaru, inda zai tatauna da takwaransa na wannan kasa Paul Biya kan batun ayyukan 'yan ta'adda na Boko Haram.

https://p.dw.com/p/1G5bZ
Hoto: GettyImages/AFP/M. Safodien

Kakakin fadar ta shugaban Najeriya ce dai Femi Adesina ya tabbatar da wannan batu, inda ya ce wannan ziyara na daga cikin tattaunawar da shugaban na Najeriya ya soma da makwabtansa kan matsalar ta Boko Haram. Bayan da aka rantsar da shi a karshen watan Mayun da ya gabata, sabon shugaban na Najeriya ya ziyarci kasashen Nijar da kuma Chadi, inda ya tattauna da shugabannin wadannan kasashe.

Ita ma wannan ziyara ta yini daya da zai kai a kasar ta Kamarun zata kasance cikin wannan sahu a kokarin da ake na hada kai domin yakar 'yan ta'addan na Boko Haram da suka addabi kasashen Tafkin Chadi a cewar Garba Shehu daya daga cikin kakakin fadar ta shugaban na Najeriya, inda ya sanar cewa sabuwar rundunar hadin gwiwar kasashen zata fara aiki ne a karshen wata ba tare da bada wani cikeken bayani ba.