1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Pakistan ya sanarda tube kakinsa na soja

November 26, 2007
https://p.dw.com/p/CTSE

Shugaban ƙasar Pakistan Parvez Musharraf ya sanarda cewa zai sauka daga mukamin babban hafsan sojojin ƙasar kuma a rantsar da shi a matsayin shugaban gwamnatin farar hula a ranar alhamis.Wannan shine karo na farko da Musharraf ya yanke ranar da zai sauka daga babban hafsan tare da maido da gwamnatin farar hula a kasar.A halinda ake ciki kuma tsofin firaministoci wato Benazir Bhutto da Nawaz Sharif sun cike takardunsu na tsayawa takara a zaben ranar 8 ga watan disamba kodayke dukkaninsu biyu sun yi barazanar janyewa daga zaɓen.A ranar lahadi Nawaz Sharif ya koma gida daga gudun hijira a kasar Saudiya.Ya ce ba zai amince da shugabancin Musharraf ba koda kuwa ƙarkashin gwamnatin farar hula.Sai kuma babu tabbacin ko gwamnati zata amincewa Nawaz Shariff shiga wannan zabe.