1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Palasdinawa malam Arafat baya cikin koshin lafiya

Mansour Bala BelloOctober 28, 2004

A yanzu anyi jungun jungun a can Gidan malam Yassar Arafat bisa rashin koshin lafiyar da take damunsa a halin yanzu .Ga dukkan alamu dai ana tattauna kaishi Asibiti a Ramallah .

https://p.dw.com/p/Bvf5
Malam Yassar Arafat shugaban palasdinawa
Malam Yassar Arafat shugaban palasdinawaHoto: AP

Babu shakka shugaban Palasdinawa malam Yassar arafat na cikin wani irin mawuyacin hali bisa rashin koshin lafiya a yau .Shugaban dai daya sha gwagwarmayar tabbatar da kasancewar yankin palasdinawa ta sami cin gashin kai daga danniyar yahudawan isreala har kawo yanzu zuciyarsa ba tai laasar ba a dangane da wannan yaki .Malam Yaassar Arafat wanda aka haife shi a shekara ta 1929 a birnin kairo can kasar masar ya kasance mutum na farko daya kafa wata kungiya ta gwagwarmayar neman yanci a shekara ta 1959 wanda kungiyar ke gabatar da ayyukanta daga can kasar kuwait .Kungiyar dai tun a shekara ta 1967 ta dauki yaki da Isreala bisa kutsen da yahudawa ke faman kaiwa yankunnan na palasdinu batare kuwa da kakkautawa ba ..A yanzu haka dai wata majiya daga can kasar Isreala tace ta sami bayanai daga mahukuntan yankin palasdinawa cewa a yau zaa dauki mAlam Arafat zuwa wani Asibiti a ramallah Tun daga daren jiya dai wasu manyan likitoci daga kasar Jordan suka isa fadar shugaban domin duba lafiyarsa .A hannu guda dai wata majiyar na cewa ya sami sauki wata majiyar kuwa na cewa har yanzu yana cikin wani hali na rashin sanin kowaye ke kansa a sabili da tsanannin ciwon dake damunsa ..Idan dai baa mantaba yau kusan shekaru ukku kenan Malam Yassar arafat ke tsare a cikin gidansa a matsayin daurin talala bisa lura ta musamman daga jamian tsaron Isreala .A hannu guda dai Isreala tace a shirye take ta bayar da damar kai Malam Yassar arafat duk inda yake bukata don neman magani sai dai kuma haR YANZU BATACE KO ZAI IYA DAWOWA BA bayan ganin likita ..Wata majiya na cewa Pm yankin na Palasdinawa ahmed Qorei ya tuntubi Pm kasar Isreala Ariel Sharon ta wayar tarho na neman fitar da Shugaba Arafat zuwa kasashen waje a halin yanzu ..A dangane da haka kuwa Pm Sharon ya amince da bukatar ta Qorei Idan dai baa mantaba Kasar Isreala tasha barazanar cewa zata kashe malam Yassar arafat ko kuma ta fattatake shi zuwa waje bisa matakan dayake dauka na tabbatar da kare martabnar yan uwansa palasdinawa wadanda ke cigaba da fuskantar matsala a hannun jamian yahudawa a yankin gabas ta tsakiya baki daya .Nabil Abu nudaina daya daga cikin masu bawa shugaba Arafat shawara yya tabbatar da cewa yana samun sauki a halin yanzu kuma nan da saonnni ukku zuwa hudu zaa tantance ko ya dace a fitar dfa shugaban zuwa wani asibiti a cikin rammallah ko kuma wajenta baki daya .