1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban palasdinawa ya nemi taimakon komitin sulhu akan izraela

Zainab A MohammadNovember 4, 2006
https://p.dw.com/p/Bu4z

Shugaba Mahmoud Abbas na yankin Palasdinawa yayi kira ga komitin sulhun mdd ,daya taimaka wajen dakatar da hare haren da dakarun Israela ke cigaba dayi a zirin Gaza.A jiya nedai sakatare general na mdd Kofi Annan yayi kira ga Izraelan data nuna halin sanin yakamata ,adangane da sabbin somame data fara yi a yankin palasdinawan wanda a jiya jumaa kadai,ya kashe palasdinawa 19.A jiyan dai mata biyu ne suka rasa rayukansu a wannan yankin,kisan da Amurka tayi nadama dashi,duk dacewa ta danganta harin izraelan da martani kann harin rokoki da palasinawan suka kai musu.