1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Siriya ya yi jawabi a majalisar dokoki

Salissou BoukariJune 7, 2016

A wani mataki na nuna wa duniya irin ci gaban da suke samu a yakin da ke wakana a kasar, Shugaba Bashar Al-Assad ya bayyana a gaban sabuwar majalisar dokokin kasar.

https://p.dw.com/p/1J1yw
Syrien Präsident Bashar al-Assad
Hoto: picture-alliance/dpa/Sana

A wannan Talata a gaban sabuwar majalisar dokokin kasar da aka zabi membobinta a zaben 'yan majalisun dokokin da ya gudana na ranar 13 ga watan Afirilu da ya gabata a yankunan da ke hannun gwamnatin kasar, inda cikin jawabin na shi Shugaba Assad ya ke cewa:

" Al'ummar Siriya ta sake bai wa duniya mamaki, bayan da ta fito dafifi ta yi zabe a lokacin zaben 'yan majalisa, musamman idan aka dubu irin yawan 'yan takaran da aka samu, duk kuwa da cewa kasar na cikin shekarunta na biyar na fama da yaki."

Sai dai 'yan adawan kasar sun ce zaben bashi da wata kima a idanun su. Hakan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sojojin gwamnati masu samun goyon bayan Rasha ke kara samun galaba kan mayakan kungiyar IS a kasar ta Siriya.