1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban sojojin Zimbabuwe ya yi murabus

Zulaiha Abubakar
December 18, 2017

Shugaban rundunar sojin kasar Zimbabuwe Constantino Chiwenga ya sauka daga mukaminsa a wani shiri na daga likkafarsa zuwa matsayin mataimakin shugaban kasa.

https://p.dw.com/p/2pbH6
Simbabwe Amtseinführung Emmerson Mnangagwa
Hoto: Getty Images/AFP/Z. Auntony

Shi dai tsohon shugaban sojojin shi ne ya jagoranci kawar da gwamnatin Robert Mugabe wanda ya shafe shekaru 37 ya na mulkin kasar ta Zimbabuwe. Jagoran sojin ya bayyana hakan ne yayin da ya ke wani jan kunne ga 'yan jam'iyyar ZANU-PF inda ya ke cewar sojojin kasar a shirye suke kowanne lokaci don murkushe kowanne irin rikici a jam'iyyar.