1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban somalia ya amince da taron sasanta tsakani

January 30, 2007
https://p.dw.com/p/BuSt

Shugaban kasar Somalia ya amince da kaddamar da wani babban taro na sasanta tsakani a kokarin kawo karshen rikicin shekaru 16 a kasar,tare kuma da nufin bada damar aikewa da dakarun wanzar da zaman lafiya na Afrika.

Bayan samun matsin lamba daga Amurka,kungiyar taraiyar turai da majalisar dinkin duniya kan wannan tattaunawar ,shugaba Abdullahi Yusuf yace gwamnatinsa a shirye take ta tattauna duk kuwa da adawa da yake samu daga jamian gwamnatinsa.

A wata ganawa da manema labarai sakataren majalisar dinkin duniya Ban Ki Moon yace dole ne tattaunawar ta hada da shugabanin kotunan musulunci da aka kora daga Mogadishu.

Shugaban na Somalia yana sa ran samun taimakon kudi na dala miliyan 20 daga kungiyar turai da karin dala miliyan 31 daga Amurka domin taimakawa dakarun AU 8,000 da ake shirin turawa zuwa Somalia.