1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Somalia yayi kira da a tura dakarun zaman lafiya a ƙasar

January 5, 2007
https://p.dw.com/p/BuVS
Shugaban Somalia Abdullahi Yusuf Ahmed yayi kira da a girke dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa nan take a cikin kasar sa. Yusuf ya fadawa taron kungiyar tuntubar juna game da Somalia wanda jami´an diplomasiya na kasashen yamma da takwarorinsu na Afirka ke halarta a birnin Nairobi cewa samun nasara kan ´yan Islama zai ba da damar wanzar da zaman lafiya a yankin baki daya. Ana kyautata zaton cewa dakarun Afirka zasu fi yawa a cikin wannan runduna ta kasa da kasa. A wani labarin kuma dakarun gwamnatin Somalia da ke samun taimakon dakarun Ethiopia sun ce suna shirin kaddamar da wani gagarumin farmaki akan sansanin na karshe na ´yan Islama dake can kudancin kasar. Wani labarin da muka samu yanzu yana cewa Ethiopia zata janye dakarun ta daga Somalia a cikin makonni biyu masu zuwa.