1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugaban Sudan yayi gargadi game da aikewa da dakarun Majalisar Dinkin Duniya

February 26, 2006
https://p.dw.com/p/Bv6g

Shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir ,yace yankin Darfur zai zama kabarin duk wasu dakarun kasashen ketare da suka shiga yankin ba tare da iznin gwamnatin kasar ba.

Wannan kalami na shi dai ya biyo bayan shiri ne na kasashen duniya su aika da dakarun Majalisar Dinkin Duniya zuwa Darfur domin hadewa da dakarun Kungiyar taraiyar Afrika(AU).

Al-Bashir ya kuma yi suka ga dakarun na AU da rashin nunwa adawa da maye gurbinsu da dakarun ma Majalisar Dibkin Duniya sukeyi.

Yace dakarun na AU zasu iya barin kasar Sudan,idan sunyi imanin cewa ba zasu iya gudanar da aikinsu na wanzar da zaman lafiya ba.