1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanci Ƙungiyar Tarayyar Turai

July 1, 2009

kamun ludayi Sweden a matsayin jagorar Ƙungiyar Tarayyar Turai

https://p.dw.com/p/If6e
Tutocin EU da SwedenHoto: DW


Ƙasar Sweden, wadda ta karɓi shugabancin karɓa karɓa na ƙungiyar tarayyar turai a wannan larabar, ta sha alwashin bayar da kariya ga ma'aikatan ofisoshin jakadancin ƙasashe mambobin ƙungiyar dake birnin Tehran na ƙasar Iran, amma kuma mahukunta a birnin na Tehran, sun zargi tarayyar turai da tsoma baki cikin harkokin cikin gidar ta, kana suka buƙaci ƙungiyar ta nemi afuwa.

Akwai yiwuwar taɓarɓarewar dangantaka tare da Iran ta kasance babban ƙalubalen da ƙasar Sweden zata fuskanta a lokacin wa'adin watanni shiddan da zata yi na shugabancin ƙungiyar tarayyar turai, yayin da kuma take ƙaunar shatawa Turai kyakkyawar hanyar warware matsalar koma bayan tattalin arziki mafi munin data faɗa ciki a shekaru masu yawa, da kuma cimma matsaya guda akan tattaunawar data shafi sauyin yanayi.

A yini na farkon daya karɓi ragamar jagorancin ƙungiyar tarayyar turai a wannan larabar, Prime ministan ƙasar Sweden, Fredrik Reinfeldt ya bayyana damuwa game da yadda lamura ke tafiya a ƙasar Iran, amma ya kawar da yiwuwar ɗaukar wani matakin gaggawa. Ya kuma ƙaryata batun cewar, ƙasashe mambobin ƙungiyar tarayyar turai, sun amince su janye Jakadunsu daga Iran, saboda tsare wasu jami'ai uku na ofishin jakadancin Birtaniya dake Tehran. Prime ministan na Sweden, ya shaidawa wani taron manema labarai domin shagalin miƙa ragamar jagorancin ƙungiyar cewar, akwai buƙatar nuna goyon baya ga ƙasar Birtaniya, amma kuma sai sun tattauna irin matakan da zasu ɗauka - ta hanyar nazarin yadda lamura ke tafiya a ƙasar ta Iran.

EU Sondergipfel in Brüssel Jose Manuel Barroso
Jose Manuel BarrosoHoto: AP

Prime minista Fredrik, ya kuma bayyana yin namijin ƙoƙari wajen kyautata matsayin tarayyar turai a idanun sauran ƙasashen duniya:

" Abu na farkon da zamu baiwa fifiko, shi ne ci, gaba da inganta martabar ƙungiyar tarayyar turai a sha'anin harkokin ƙetare, a yanayin ƙasa da ƙasar da nake ganin akwai ƙaruwar buƙatu waɗanda kuma ke da matuƙar wahala."

A lokacin da yake yin jawabi na haɗin gwiwa ga manema labarai, tare da shugaban hukumar tarayyar turai, Jose Manuel Barroso, Prime ministan Sweden, ya ce ƙasarsa zata ɗauki matakan shawo kan matsalar rikicin tattalin arzikin da duniya ke fama da ita, da kuma na sauyin yanayi, ta hanyar kammala shirye shiryen tinkarar babban taron majalisar ɗinkin duniya akan sauyin yanayi, wanda za'a yi a Copenhagen na ƙasar Denmark.

Mahukunta a birnin Stockholm na ƙasar Sweden dai, na son ƙasashen ƙungiyar tarayyar turai su sanya hannu akan yarjejeniyar da ɗaukacin ƙasashen duniya zasu cimma a Copenhagen cikin watan Disambar wannan shekarar, wadda zata maye gurbin yarjejeniyar ɗumamar yanayi ta Kyotor da wa'adinta ke ƙarewa a shekara ta dubu biyu da goma sha biyu.

Der schwedische Ministerpräsidenten Fredrik Reinfeldt (Ausschnitt)
Fredrik ReinfeldtHoto: picture-alliance/dpa

Sisiliya Manstrum, ita ce ministar dake kula da lamuran da suka shafi tarayyar turai a ƙasar Sweden:


" Manyan abubuwan guda biyun da zamu sanya a gaba, su ne matsalar koma bayan tattalin arzikin dake addabar duniya, da kuma sauyin yanayi."

Sauran abubuwan da wa'adin jagorancin Prime ministan na Sweden zai bada fifiko akansu kuwa, sun haɗa da inganta tsarin shari'a a nahiyar Turai, da kuma faɗaɗa ƙungiyar, wadda a yanzu ke da ƙasashe mambobi ashirin da bakwai.


Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Zainab Mohammed