1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin Amurika 44

November 26, 2010

Daga samun yancin kan Amurika zuwa yanzu, shugabani 44 su ka yi jagorancin ƙasar

https://p.dw.com/p/QJa2
Sugabanin Amurika na farko da na yanzuHoto: AP

 Amurika ta yi shugabani 44 daidai.

 Shugaban Amurika na farko wanda shine ya yi gwagwarmayar ƙwato ƙasar daga mulkin mallakar turawan Birtaniya, shine Georges Washington, wanda ya yi mulki daga 1789 zuwa 1792.

Na biyu shine Jeorges Adams, wanda a zamanin shugaban farko shine mataimakin shugaban ƙasa.Ya yi mulki daga 1797 zuwa 1801.

Na ukku Thomas Jefferson wanda ya yi mulki daga 1801 zuwa 1809.

Shugaba na huɗu shine James Madison wanda ya yi mulki daga 1809 zuwa 1817.Tarihin ya rike cewar shine tushen kudin tsarin mulkin Amurika.

Sai kuma James Monroe wanda shine shugaban ƙasar Amurika na biyar.Ya yi mulki daga 1817 zuwa 1825.

Na shidda shine shugaba John Q.Adams, wanda shi da ne ga tsofan shugaban ƙasa Jeorges Adams.Ya yi mulki daga 1825 zuwa 1829.Ya yi suna matuƙa ta fannin yaƙi da bautar da Amurika baƙar fata.

Shugaban ƙasar Amurika na bakwai shine Andrew Jackson wanda ya hau karagar mulki daga 1829 zuwa 1837.

Sai na takwas wato Martin van Buren, wanda ya mulki Amurika daga 1837 zuwa 1841.

Shugaba na tara shine Williams H.Harrison duka-duka watan shi guda kan karagar mulki ya mutu sanadiyar rashin lafiya.

 Shugaban Amurika na goma shine John Tyler daga 1841 zuwa 1845.

Mai bi masa shine James K.Polk daga 1845 zuwa 1849.

A lokacin mulkinsa Amurika ta samu yawa girman ƙasarta na yanzu.

Shugaba na 12 shine Zachary Taylor shima ya mutu bayan watani 16 kawai na mulki.

Shugaba na 13 shine Millard Fillmore daga 1850 zuwa 1853.

Sai kuma wanda ya gaje sa mai suna Franlin Pierce 1853 zuwa 1857.

Shugaba na 15 shine James Buchanan daga 1857 zuwa 1861.

Shugaban ƙasar Amurika na 16 shine Abraham Lincoln daga 1861 zuwa 1865.Shine shugaban farko na Jam´iyar Republican.Kuma a lokacinsa ne aka ƙaddamar da dokar haramta bauta a Amurika.

An kashe shi cikin harin ta´addanci a shekara 1865.

Bayan shi sai Andrew Johnson daga 1865 zuwa 1869.

Bayan shi sai Ulysses S.Grant daga 1869 zuwa 1877.

Shugaban Amurika na 19 sunan sa Rutherford B.Hayes daga 1877 zuwa 1881.

Na 20 shine James A.Garfield wanda watani shida kacal ya yi kan mulki aka hallaka shi.

Sai kuma shugaba na 21  Chester A.Arthur wanda ya yi mulki daga 1881 zuwa 1885.

Sai kuma shugaba na 22 wato S.Grover Cleveland .Ya yi mulki daga 1885 zuwa 1889.

Mai bi masa shi ne Benjamin Harrisson.Kakansa William Harrison ya taɓa yin shugaban ƙasa.

Shugaban ƙasar Amurka na 24 shi ne S.GRover Cleveland, shugaba na 22, shi ne ya sake dawowa.

Mai bi masa shi ne William McKinley daga 1897 zuwa 1901.

 Amurika ta zaɓi Theodore Roosvelt a matsayin shugaba na farko a cikin ƙarni na 20.Ya yi mulki daga 1901 zuwa 1909.

Mai bi masa shi ne William H.Taft wanda ya yi shekaru takwas kan karagar mulki.

Shugaba na 28 shi ne T. Wilson daga 1913 zuwa 1921.

Shi ne ya saka Amurika cikin yaƙi duniya na ɗaya, kuma  a lokacinsa ne matan Amurika su ka samun yancin zaɓe.

Shugaban ƙasar Amurika na 29 sunansa Warren G. Hardind, ya rasu a cikin shekarunsa uku kan mulki.

Wanda ya gaje sa sunansa J.Calvin Coolidge.

Sai kuma shugaba na 31 mai suna Herbert C.Hoover daga 1929 zuwa 1933.

Ɗaya daga shugabanin da su ka yi suna a Amurika shi ne Franklin Delano Roosvelt, wanda a zamanin sa ne aka gwabza yaƙin duniya na biyu,Kuma shine tushren girka Majalisar Ɗinkin Duniya.Ya rasu gap ga ƙarshen wannan yaƙi

Wanda ya gaje sa shine Harry S. Truman, wanda ya hau mulki daga 1945 zuwa 1953.wani mummunan tasiri da ya bari a matsayin tarihi shine yin amfani da makamai masu guba  a ƙasar Japan a biranen Hiroshima da Nagazaki, wanda kuma daga nan ne ƙasashe masu ƙawance da Amurika su ka ci yaƙin duniya na biyu.Kuma ƙasashen Turai ba za su taba mantawa da shi ba, saboda bayan yaƙin shine ya bada wani tallafin kuɗi da aka raɗawa suna Plan Marshall domin sake gina Turai wada yaki ya kacakaca da ita.

Shugaban ƙasar Amurika na 34 shine Eisenhower daga 1953 zuwa 1961.

Bayan shi sai John F.Kennedy wanda ya yi mulki daga 1961 zuwa 1963.Mutanen Jamhuriya Nijar ba za su manta ba da shi ba,domin shi ne ya gina gadar nan da ta haɗa  birnin Yamai da unguwar haro banda.

Shi ma shugaba Kennedy an kashe shi ne kamin cikar wa´adin mulkinsa.

Lyndon B.Johnson ya gaje shi inda yayi shekaru huɗu.

Shugaba na 37 sunansa Richard M.Nixon.Ya yi murabus daga wannan muƙami a shekara 1974, jim kaɗan bayan da yan majalisa su ka shiga yunƙurin tsige shi.

Gerald Ford R. Ford ya gaje shi daga shekara 1974 zuwa 1977.

Sai kuma shugaba na 39, James Jimmy Carter wanda har yanzu da ransa ya na jagoranta wata ƙungiyar bada agaji ta Jimmy Carter Fundation.

Bayan shi sai Ronald Regan daga 1981 zuwa 1989.Maitaimakinsa George H.W.Bush ya gaje sa daga 1989 zuwa 1993.

Daga shi sai Bill Clinton daga 1993 zuwa 2001.

Sannan sai Georges W.Bush ɗan geroge Bush tsofan shugaban ƙasa.

Sai kuma mai shugaba mai ci yanzu Barack Obama, wanda shine shugaban Amurika na 44.

Mawallafi: Yahouza Sadisou Madobi

Edita: Zainab Mohamed Abubakar