1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin duniya sun laánci harin taáddanci a Masar

April 25, 2006
https://p.dw.com/p/Bv0e

Shugabannin ƙasashe na duniya na cigaba da yin Allah wadai da hare haren bama bamai da suka auku a wurin yawon bude idanu na Dahab dake ƙasar Masar wanda ya yi sanadiyar mutuwar a ƙalla mutane 23 tare da jikata wasu mutanen da dama. P/M ƙasar Australia John Howard, yace harin wata alama ce dake nuni da cewa harin taáddanci bai bar kowa ba, a saboda haka yace akwai bukatar ɗaukacin kasashe na duniya su kara ƙaimi wajen yaƙi da ayyukan taáddanci a doron kasa. Shugaban ƙasar China Hu Jin tao wanda ke ziyarar ƙasashen larabawa ya baiyana ƙudirin ƙasar sa, na haɗa hannu da gamaiyar ƙasa da ƙasa, tare da ƙasar Masar, wajen yaƙi da taáddanci. A nasa bangaren, Shugaban Amurka George W Bush ya baiyana harin da cewa tsabar rashin Imani ne. Har ya zuwa yanzu babu wanda ya baiyana lhakin kai wannan hari, sai dai Jamián tsaro na cigaba da bincike domin gano waɗanda ke da hannu harin taáddancin.