1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabanin Larabawa sun ce bai kamata Sudan ta rabu ba

October 11, 2010

Shugabannin Libya da Saudiyya sun ce ƙasashen Afirka da na Larabawa, su haɗa kai wajen samar da zaman lafiya a Sudan

https://p.dw.com/p/Pavj
Gaddafi da Al-BashirHoto: AP

Shugabannin Libya da Saudiyya, sun nuna rashin amincewarsu da raba ƙasar Sudan, a taron ƙolin ƙasashen Afirka da na Larabawa na biyu, wanda aka gudanar a Libya ranar Lahadi.

Shugaban Libiya, Muammar Gaddafi wanda ya karɓi baƙoncin taron na farko cikin shekaru 30 da suka gabata, ya ce rabuwar Sudan, za ta iya yaɗuwa a tsakanin ƙasashen Afirka, kuma ka iya zama abun koyi ga ƙasashen da suka daɗe suna fama da rigingimun cikin gida. Shi ma ministan harkokin wajen Saudiyya, Saud Al-Faisal ya ce a ra'ayin sa, yin hakan ba zai haifar da ɗa mai ido ba, kuma ya yi kira ga ƙasashen nahiyoyin biyu, da su haɗa kai wajen shawo kan lamarin, saboda duk sakamakon da aka samu, zai shafi yankunan gaba ɗaya.

Kamfanin dillancin labaru na Sudan SUNA ya rawaito cewa, shugaba Omar Al Bashir, wanda ya halarci taron, ya faɗawa manema labaru cewa akwai batutuwa kamar raba kan iyakokin yankunan, tantance 'yan ƙasa waɗanda za su kaɗa ƙuri'a da matsalar ruwa waɗanda dole a fayyace kafin a kaɗa ƙuri'ar raba gardama a watan Janairu. Shugaban kudancin ƙasar Salva Kiir ya sha alwashin sai an gudanar da ƙuri'ar.

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu

Edita: Mohammad Nasiru Awal