1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Afirka sun halarci bukin rantsar da al-Bashir

May 27, 2010

Al-Bashir ya yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙi a Sudan a lokacin wa'adin mulkin sa na wasu shekaru biyar

https://p.dw.com/p/NazC
Hoto: picture alliance / abaca

A yau Alhamis ne aka rantsar da Omar Hassan al-Bashir a matsayin shugaban ƙasar Sudan a zaɓen farko cikin shekaru 24.

Al-Bashir, wanda shi ne shugaban ƙasa ɗaya tilon da ke kan gadon mulki da kotun hukunta masu aikata laifuffukan yaƙi ke tuhuma da laifin cin zarafin jama'a ta hanyar kissar gilla zai jagoranci jefa ƙuri'ar raba gardamar da za'a kaɗa a watan Janairu game da ɓallewar yankin kudancin sudan. Ana sa ran wannan ƙuri'ar ce ce za ta ba ynkin, wanda ke da arziƙin man fetur yancin kan sa.

Shugaban ya marabci shugabanin ƙasashen Afirka da dama waɗanda suka haɗa da na Mauritania, Chad da Djibouti, inda ya faɗa wa mahalarta shagalin rantsarwar cewar ba za a sake koma wa ga wani yaƙi ba, kana sabon mulkin nasa zai mai da hankali wajen kyautata harkokin tsaro da daidaituwar lamura a ƙasar.

An haifi Bashir a shekarar 1944 a yankin kogin Nilu da ke arewacin Khartoum babban birnin ƙasar. Mahaifin sa kuma manomi ne kuma yayi karatu a makarantar sojojin Sudan a 1966 bayan nan, ya cigaba da aikin soja har ya kai muƙamin Janar.

Shugaban ƙasar ya yi alƙawarin cewa zai kawo ƙarshen rikicin Darfur ta hanyar ƙulla yarjejeniya domin inganta dangantakar sa da kudancin ƙasar

Ƙungiyar tarayyar turai tana goyon bayan tuhumar da kotun hukunta masu aikata manyan laifukan yaƙi ke yi masa, amma tana so a cigaba da tattaunawa har sai an tabbatar da cewa ƙuri'ar raba gardamar ba ta haddasa wani tashin hankali ba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Halima Balaraba Abbas