1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin duniya na juyayin mutuwar Helmut Kohl

Zainab Mohammed Abubakar
June 17, 2017

Sakonnin ta'aziyya daga shugabannin gwamnatoci da kasashen duniya da ma 'yan siyasa na ci-gaba da kwarara zuwa Jamus dangane da mutuwar tsohon shugaban gwamnati Helmut Kohl

https://p.dw.com/p/2ereO
Helmut Kohl Bad in der Menge
Hoto: Picture-alliance/dpa/H. Hollemann

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana marigayi Helmut Kohl da kasancewa babbar sa'a da Jamus ta taba samu, mutumin da ake yiwa ikirarin jagoran hadin kasan kasar. A wata ganawa da tayi da paparoma a wannan Asabar, Merkel ta ce jagoran darikar roman katolika na duyar ya mika mata sakonsa na ta'aziyya.

" Na samu damar ganawa da da Paparoma a yau, a matsayi na na mai zama mai masaukin bvakin taron kasashe masu cigaban masana'antu na G20 a birnin Hamburg. Da farko ya mika ta'aziyyarsa dangane mutuwar Helmut Kohl, tare da bayyana shi da kasancewa dottijon da Jamus bazata taba mantawa da shi ba".

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya bayyana tsohon shugaban gwamnatin na Jamus a matsayin tushen kyakkyawar dangantakar amintaka tsakanin kasashen Jamus da Faransan.

Altbundeskanzler Helmut Kohl
Helmut KohlHoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Jagoran hadakar cigaba na Poland Lech Walesa ya jinjinawa Kohl, tare da bayyana shi da kasancewa daya daga 'yan siyasa masu basira a duniya.

"Mun san juna sosai saboda mun yi alaka a lokuta daban daban daban. Zan iya cewa mun samu fahintar juna da shi, kamar yadda 'yan Poland suke da Jamusawa. Duk da haka mukan cimma daidaituwa kan batutuwa da suka shafi Turai , yadda zamu inganta hadin kan turai. Ko shakka babu shugaba ne na kasar da ta fi kowacce karfin tattalin arziki a turai, yana da nashi ra'ayi amma duk da haka manufa guda ce muke da ita"

A headgwatar kungiyar Tarayyar Turai da ke birnin Brussels din kasar Beljium dai an sauke tutocin kasashe a harabar hukumar gudanarwata zuwa rabi, tun bayan barkewar labarin mutuwar Helmut Kohl a ranar Juma'a, domin karramashi.

Akasarin 'yan siyasa na bayyanashi da zama mutumin da yayi ruwa yai tsaki wajen tabbatar da sake hadewar yankunan yammaci da gabashin Jamus a shekara ta 1990, kuma wanda ya zame a bun koyi ga shugabar gwamnati ta yanzu Angela Merkel.

Jaime Andres dan kasar Spain ne:

Helmuth Kohl Grundsteinlegung Bundeskunsthalle Bonn 1989
Helmut Kohl a shekara ta 1989Hoto: picture-alliance/dpa/T. Brakemeier

" Zan iya tuna wani lokaci a wani gidan talabijin na Faransa, inda wani matashin Bafaranshe ya tambayeshi , me ya sa Turai zata cigaba da kafuwa" sai ya ce: ba ka taba ganin yaki a wannan nahiya ba, kuma ba zaka taba sanin yaki ba. Don haka a ganina wannan shine abun da mafi muhimman da shugaban gwamnti Kohl ya bari abun tuni"

Ita kuwa Elizabeth Willocks daga Birtaniya cewa tayi:

" Ya kasance dottijo, ya kawo hadin kai na Jamus, kuma zamu cigaba da tunashi bisa wannan".

Jaridun Jamus dai sun ruwaito cewar tsohon shugaban gwamnati Helmut Kohl ya mutu ne a ranar Juma'a da misalin kiarfe 9 da kwata na safe, a kan gadonsa a mahaifarsa da ke Ludwigshafen a yankin yammavcin Jamus.

Za'a jima a juyayin mutuwar Kohl a fagen siyasar duniya saboda irin gwagwarmayarsa da rasyaw da ya taka bawai anan tarayyar Jamus ba harda Turai dama duniya baki daya.