1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabannin Eu sun fara taron kolin su

December 15, 2005
https://p.dw.com/p/BvGK

Da yammacin yau ne shugabannin kungiyyar gamayyar Turai, wato Eu suka fara gudanar da wani taron kolin kungiyyar a birnin Brussels na kasar Belgium.

Ajandar taron na wannan lokaci dai shine na cimma matsaya guda game da kasafin kudin kungiyyar na shekaru bakwai masu zuwa a nan gaba.

Ya zuwa yanzu dai kusan shawarar da kasar Biritaniya ta kawo na kokarin warware wannan matsala ya samu suka daga wasu kusoshin kungiyyar na Eu wato kasar Faransa da Jamus.

Wannan dai shawara ta Biritaniya, na bukatar kara yawan kasafin kudin da kungiyyar ke kashewa,wanda hakan zai bada damar karin kudi ga sabbin mambobin kungiyyar, kana a daya hannun kuma da kin rage wani abu daga cikin kason harajin da kungiyyar take mayarwa kasar ta Biritaniya.

Ya zuwa yanzu dai shugabannin kungiyyar ta Eu na daga yanzu izuwa watan maris, su kammala duk wata tattaunnawa da zasu yi don warware wannan takaddama.