1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Angela Merkel ta Jamus ta fara ziyara a Brazil

Yusuf BalaAugust 20, 2015

Batun yaki da sauyin yanayi da satar bayanai ta kafat intanet na cikin abubuwan da zasu dauki hankali a wannan ziyara.

https://p.dw.com/p/1GI8O
Deutschland IFA in Berlin Angela Markel
Shugaba Angela MarkelHoto: AP

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Markel ta isa Brazil a ziyarar da ta fara ta kwanaki biyu tare da wasu mambobin majalisar zartarwarta inda zasu tattauna da shugaba Dilma Rousseff kan batutuwa da suka shafi sauyin yanayi da batutuwa da suka hadar da tsaron bayanai a shafukan intanet.

Irin wannan tattaunawa dai na zama irin ta farko da bangarorin gwamnatin daga kasashen Turai da Amirka ta Kudu da tattalin arzikinsu ya banbanta da saura a yankunansu zasu zauna kan wannan batu.