1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shugabar Jamus ta nemi karin waadin dakarun kasar a Afghanistan

September 15, 2007
https://p.dw.com/p/BuBL

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sake neman goyon bayan kara waadin aiyukan dakarun Jamus a kasar Afghanistan.merkel tayi ikrarin cewa ba jamaar kasar Afghnistan kadai aiyukan sojojin Jamus yake taimakawa ba har ma da tabbatar da tsaron kasar ta Jamus.A cikin wattannin oktoba da nuwamba majalisa dokoki ta Bundestag zata yi muhawara kann karawa dakarun na Jamus waadin aikinsu a Afghanistan.A halinda ake ciki kuma jamiyar adawa ta Greens ta bukaci wakilanta a majalisar da kada su bada goyon bayansu ga aiyukan dakarun Jamus a Afghansitan.wajen wani babban taronta na musamman jamiyar Greens ta amince da wani kuduri na kin amincewa da aiyukan dakarun Jamus din muddin dai ya shafi fada ko yaki da yan taliban.

Gwamnatin Angela Merkel bata dogara kann kuriun yan adawa ba game da wannan batu.