1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

shugabar Jamus tace zata rage yawan dogon turanci a cikin harkokin kungiyar

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butp

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta sanarda shirinta na rage yawan dogon turanci na Kungiyar Taraiyar Turai a lokacinda Jamus zata karbi shugabancin karba karba na kungiyar a 2007.

Da take jawabi wajen babban taro na kungiyar a Brussels,Merkel tace tana da zummar tattauna hanyoyin farfado da batun kundin tsarin mulkin kungiyar cikin shekaru 2 masu zuwa.

A jiya alhamis shugabannin kungiyar suka amince da waadin 2008.

Kasashen Faransa da Holland a shekarar data gabata sun jefa kuriar kin amincewa da kundin na turai.

Wasu batutuwa kuma da taron na kwanaki 2 ke tattaunawa akansu sun hada da manufar bakin ketare da kuma fadada kungiyar.