1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shugabar Liberia na shiga tsakani a rikicin Libya da Nijeriya

April 1, 2010

Ƙasashen Libya da Nijeriya sun gaza warware taƙaddamar dake tsakaninsu duk da sanya bakin da shugabar Liberia ta yi

https://p.dw.com/p/Mjjj
Muƙaddashin shugaban Nijeriya Goodluck JonathanHoto: AP

Shugabar ƙasar Liberia Ellen Johnson - Sirleaf, wadda ke ƙoƙarin shawo kan taƙaddamar data kunno kai a tsakanin Nijeriya da ƙasar Libya, ta gana tare da muƙaddashin shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan da kuma Jakadan Libya a Nijeriya, jiya laraba. Sai dai kuma basu cimma maslaha ba a lokacin ganawar. Wannan taƙaddamar, ta zo ne bayan da shugaban Libya Mua'mmar Gaddafi ya bayar da shawarar raba Nijeriya i zuwa ɓangarori biyu tsakanin Muslmai da Kirista - a matsayin hanyar warware tashe - tashen hankular dake addabar ƙasar, shawarar da kuma ta janyo Allah wadai daga al'ummmomin Nijeriya daban daban. A sakamakon hakane kuma, Nijeriya ta kira Jakadanta a ƙasar Libya ya dawo gida.

A wannan makon ne kuma, Gaddafi ya sake yin kira ga rarraba Nijeriya zuwa ƙasashe da dama saoda yawan ƙabilun da yace, ƙasar ke dasu.

Wani kakakin fadar shugaban Nijeriya Ima Niboro, ya shaidawa manema labarai cewar, ko da shike ganawar shugabar Liberia da muƙaddashin shugaban Nijeriya bata kaiga warware matsalar ba, mataki na gaba shi ne cewar, za'a ci gaba da gudanar da taron, har sai Nijeriya da Libya sun cimma maslaha a tsakaninsu.

Niboro, ya ƙara da cewar, mukaddashin shugaban Nijeriya ya fito fili ya bayyana buƙatar shugabannin wasu ƙasashe su bi tafarkin diflomasiyya a irin furucin da suke yi game da wasu ƙasashen, yana mai cewar, akwai furucin da ka iya tada jijiyar wuya.

Sai dai kuma, bayan taron, shugabar Liberia, da kuma mambobin tawagar ƙasar Libya sun ƙi cewa uffan game da taron. Ba'a san wani lokaci ne za'a sake gudanar da taro akan batun ba.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh

Edita: Umaru Aliyu