1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sin: Azaba

December 2, 2005

Majalisar Dinkin Duniya ta gudanad da wani bincike a kasar Sin, inda ta gano cewa, har ila yau ana matukar azabtad da fursunoni a kasar, fiye da yadda ake zato.

https://p.dw.com/p/Bu3i
Alamar azaba.
Alamar azaba.Hoto: AP

Manfred Nowak, shugaban tawagar binciken zargin azabtad da fursunoni na Majalisar Dinkin Duniya, wadda ta kammala ziyarar aikinta a kasar Sin, ya ba da sakamakon binciken da suka gudanar, inda ya bayyana cewa babu shakka, a kasar ana azabtad da fursunoni fiye da yadda ake zato. Musamman wadanda suka fi shan azaba a hannun jami’an tsaro, sun hada ne da `yan tsirarun kabilun kasar, da mabiya darikar nan ta Falungong da kuma masu fafutukar neman sauyi a harkokin siyasar kasar.

A wani taron mameman labarai da tawagarsa ta kira a birnin Shanghai yau, Manfred Nowak ya bayyana cewa:-

„Sakamakon wucin gadin da zan iya bayarwa shi ne: a cikin `yan shekarun baya bayan nan, an sami ragowar yawan mutanen da ke daukaka karar an azabtad da su a gidajen yari a Sin. Amma, wadannan alkaluman sun shafi gidajen yari a manyan birane ne kawai. Ban sami damar ziyarar gidajen yari da dakunan kurkuku na `yan sanda a yankunan karkara, don gudanad da bincike ba.“

Tawagar da Manfred Nowak ya jagoranci dai, ta shafe makwanni biyu tana ziyarar sansanonin da aka tsare fursunoni a biranen Beijing, da yankin Tibet da kuma jihar nan ta Xinjiang, inda musulmi suka fi yawa. Wannan dai shi ne karo na farko da wata tawagar Majalisar Dinkin Duniya ta sami izinin kai ziyara a gidajen yari da na horad da masu aikata laifuffuka a kasar ta Sin. A ganin shugaban tawagar, Dennis Nowak:-

„Ma’anar da kasar Sin ke bai wa kalmar azaba ta bambanta da ta gamayyar kasa da kasa. A Sin, sai mutum ya ji rauni, a hannun jami’an tsaro, wanda kuma za a iya gani a jikinsa ne, za a ce an azabtad da shi. Amma duk wata galllaza wa mutum da za a yi, wadda za ta shafi hankalinsa ta sa shi cikin wani mummunan hali, ko kuma wadda ba za a iya ganin alamunsu a jikinsa ba, ta ba azaba ba ce, bisa ma’anar da hukumar kasar Sin din ke bai wa kalmar azaba.“

Shi dai wakilin na Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci hukmar kasar Sin din da ta ba da alkaluman mutanen da ta yanke musu hukuncin kisa a kasar. Kasar Sin dai, ita ce kasar da ta fi ko wacce yanke wa al’ummanta hukuncin kisa a duniya. Har ila yau babu wanda ya san yawan mutanen da ake zartad da hukuncin kisa a kansu a kasar a ko wace shekara. Manfred Nowak, ya ce ya sami damar yin doguwar tattaunawa da manayn jami’an shari’ar kasar, kuma ma’aikatar harkokin wajen Sin din ta ba shi cikakken goyon baya. Amma a lokacin gudanad da bincikensa, bai sami damar tafiyad da aikinsa kamar yadda ya kamata ba. Ko’ina, sai an hada shi da jami’an sa ido, mafi yawansu kuwa, `yan leken asirin kasar ne ko kuma `yan sanda. Ya kuma kara da cewa, a lokuta da dama, fursunonin sun dari-dari wajen amsa tambayoyinsa, saboda tsoron da suke yi na abin da zai auku bayan tafiyarsu. Kai tsaye ma wasu suka ki magana da shi. Har ila yau dai, inji jami’in, an hana `yan tawagar shiga da kyamara don daukar hoto a gidajen yarin da suka ziyarci.

Tawagar dai ta yi kira ga gwamnatin kasar ta Sin da ta kawo karshen matakan da ake dauka kan mutanen da ake tsare da su, wai na ba su horon kirki. Kazalika kuma, ya yi kakkausar suka ga yadda ake wulakantad da, wadanda aka yanke musu hukuncin kisa, inda a ko yaushe daddaure su ake yi da sarkoki. A karshe dai jami’in na Majalisar Dinkin Duniya ya nemi mahukuntan kasar Sin da su kafa cibiyoyin kula da kare hakkin bil’Adama a duk fadin kasar.