1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Amirka ta yi barazanar daukar matakin soja

Ramatu Garba Baba
March 13, 2018

A yayin da Amirka ke cewa za ta dauki matakin anfani da karfi a rikicin Siriya, fararen hula da aka yi nasarar kwashe wa daga birnin Ghouta sun koka kan yadda rikicin ya raba su da 'yan'uwansu.

https://p.dw.com/p/2uDLt
USA UN Sicherheitsrat Nikki Haley
Hoto: picture-alliance/newscom/J. Angelillo

Daruruwan jama'a da aka yi nasarar kwashe wa ake kuma tsugune da su a wani sansani sun baiyana damuwa kan halin da sauran 'yan'uwan da suka baro ke ciki. An kwaso akasarin su a yayin da hare-hare ta sama ke tsananta a birnin, da kuma zargin cewa dakarun gwamnati na anfani da wasu makamai masu guba kan al'umma a kokarin karbe karfin iko daga 'yan tawaye.

Wannan ya sa a wata sanarwa da Amirka ta fitar a jiya Litinin, ta yi barazanar daukar mataki na anfani da karfin soja don kawo karshen abin da ta kira cin zarafi da anfani da makami mai guba kan farraren hulan da ba su ji ba ba su gani ba. Amirka ta gabatar da wani daftarin kudiri a gaban kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya na nema a tsagaita barin wuta a Siriyan.

Jakadiyar Amirka a majajalisar Nikki Haley wacce ta bayyana kudirin, ta soki lamirin Rasha da Siriya da gaza aiwatar da yarjejeniyar dakatar da bude wutan da aka cimma a makonin da suka gabata.