1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Sojojin gwamnati sun kwace Ghouta

Salissou Boukari
April 15, 2018

Rundinar sojojin Siriya ta sanar da karbe iko da illahirin yankin gabashin Ghouta da ke kusa da birnin Damas daga hannun 'yan tawayen kasar, bayan fitar da mayaka na karshe daga birnin Douma.

https://p.dw.com/p/2w4Cn
Syrien Staatliche Polizeieinheiten übernehmen Douma
'Yan sandan Siriya a Yankin gabashin GoutaHoto: picture alliance/AP Photo/SANA

Wannan sanarwa na a matsayin babbar nasara ga gwamnatin ta Shugaba Bashar Al-Assad, kuma na zuwa ne 'yan awoyi bayan da kasashen Amirka, Faransa da Britaniya suka yi lugudan wuta a wasu mahimman wurare uku na gwamnatin ta Siriya, a wani mataki na martani kan zargin da ake yi wa gwamnatin da amfani da makami mai guba kan 'yan tawaye abirnin Douma.

Kamfanin dillancin labaran kasar ta Siriya na SANAA, ya rawaito kalaman wani babban jami'in sojan kasar na cewa sun kakkabe 'yan ta'adda daga yankin gabashin Ghouta gabaki daya. Samamen da sojojin gwamnatin ta Siriya masu samun goyon bayan Rasha suka ayyana a yankin na Ghouta na kusan watanni biyu, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1.700 a cewar kungiyar nan da ke sa ido kan kare hakin bil-Adama a kasar ta Siriya.