1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya ta yi watsi da tayin tsagaita wuta a Aleppo

Gazali Abdou Tasawa
December 8, 2016

Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya yi watsi da tayin da 'yan tawayen kasar suka yi masa na tsagaita wuta a birnin Aleppo domin bai wa fararan hula damar ficewa daga birnin.

https://p.dw.com/p/2Tw6e
Syiren Präsident Bashar al-Assad Interview
Hoto: Reuters

Shugaban Siriya Bashar al-Assad ya yi watsi da tayin da 'yan tawayen kasar suka yi masa na tsagaita wuta a birnin Aleppo, tare ma da bayyana cewa nasarar dakarunsa a birnin ce za ta kasance wani babban tsani ga kawo karshen yaki a kasar baki daya.

 

'Yan tawayen kasar ta Siriya wadanda dakaran gwamnatin Assad ke daf da fatattaka daga birnin na Aleppo suka yi tayin tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyar domin a cewar su bai wa fararan hula wadanda yaki ya rutsa da su a cikin birnin damar ficewa. 

A yammacin jiya Laraba ma dai manyan kasashen duniya da suka hada da Amirka da Faransa da Ingila, Rasha dama Jamus sun tattauna kan batun tsagaita wutar a Aleppo a wani taro da suka shirya a birnin Hamburg na kasar Jamus ba tare da cimma wata matsaya ba, bayan da aka kasa samun fahimtar juna musamman tsakanin John Kerry na Amirka da takwaransa na Rasha Sergei Labrov.