1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: 'Yan tawaye sun amince da tsagaita wuta

Gazali Abdou TasawaFebruary 26, 2016

A cikin wata sanarwa da ya fitar kwamitin kawancan kungiyoyin 'yan tawaye da 'yan adawar Siriya 97 ya sanar da mutunta yarjejeniyar tsagaita wutar da za ta soma aiki a 12 na daren wannan Jumma'a

https://p.dw.com/p/1I2vP
Syrien Waffenruhe wird von Rebellen und Regierung nicht eingehalten 26.10.12 Damaskus
Hoto: Reuters

A lokacin da ya rage 'yan awoyi yarjejeniyar tsagaita wuta a yakin Siriya ta soma aiki, kungiyoyin tawaye kasar ta Siriya kimanin dari sun sanar da ba da hadin kansu ga shirin.A cikin wata sanarwa da ya fitar a wannan Jumma'a kwamitin koli mai kula da tattaunawa wanda ya kunshi manyan kungiyoyin 'yan adawa da na 'yan tawayen Siriya ya tabbatar da wannan matsayi nasa na mutunta matakin tsagaita wutar na wa'adin makonni biyu da zai soma aiki a karfe 12 na daran wannan jumma'a.

Daga nashi bangare Shugaba Rasha Vladmir Poutin ya sanar a wannan Jumma'a cewar ko da yake babu wata hanya mafi a'ala ta kawo karshen rikicin Siriyar kamar ta sulhu amma kuma ya ce lamarin zai matukar wahala.

Sai dai kuma ya jaddada matsayinsa na ci gaba da yakar Kungiyoyin IS da na Al-Nosra wadanda matakin tsagaita wutar bai shafesu ba.