1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasa a Rasha na fuskantar sabon salo

Ibrahim SaniDecember 18, 2007
https://p.dw.com/p/Cd24

Shugaba Vladimir Putin na Russia ya amince daya zamo Faraministan ƙasar, bayan ƙarewar wa´adin mulƙinsa. Hakan zai tabbata ne a cewar Putin, Idan ɗan takarar Jam´iyyarsu ta URP ya lashe zaɓen shugaban ƙasar. Tuni dai Mr Putin ya zaɓi Dmitry Medvedev, a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasar ƙarƙashin Jam´iyyar ta URP. Mr Dmitry ya kasance tsohon manajan yaƙin neman zaɓe ne na shugaba Putin, kuma a yanzu haka na hannun damansa. Kundin tsarin mulƙin Russia dai ya hanawa Mr Putin yin tazarce a karo na uku a jere. Sabon muƙamin na Mr Putin in har ya tabbata, zai bashi damar ci gaba da taka muhimmiyar rawa a fagen siyasar ƙasar.