1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siyasar Habasha ya ja hankalin jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
February 23, 2018

Murabus da shugaban gwamnatin Habasha da tsaurara dokar ta-baci, da rashin sanin tabbas kan maye gurbin Firamista Hailemariam Desalegn, sun kara tsananta rikici a kasar.

https://p.dw.com/p/2tDqn
Äthiopien Ministerpräsident Hailemariam Desalegn kündigt Rücktritt an
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta yi tsokaci kan halin da ake ciki a kasar Habasha bayan murabus din Firaminista Desalegn Hailemariam a makon da ya gabata, jaridar ta fara ne da cewa Habasha ta mayar dokar ta-baci wani lamari da aka saba da shi. Ta ce murabus din da shugaban gwamnatin kasar ya yi da tsattsaurar dokar ta-baci da rashin sanin tabbas a gwagwarmayar neman rike madafun a tsakanin 'ya'yan jam'iyyar kawance ta EPRDF da ke jan ragamar mulki sun kara tsananta rikici a kasar wadda da ma aka santa da zama karkashin mulkin kama karya. Jaridar ta ce rikicin da Habasha ta tsunduma ciki tun farkon boren gama gari na adawa da gwamnati shekaru biyu da suka wuce, yanzu haka ya kai ga jagororin kasar. Dole ne jam'iyyar ta EPRDF ta yi wa kanta kwaskwarima matukar ba ta son ta rasa iko da kasar. Amma bisa ga dukkan alamu da jan aiki gabanta.

Äthiopien Polizei
'Yan sandan Habasha kenan ke sintiri a birnin Addis AbabaHoto: imago/Xinhua

Ita ma jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung, ta buga labari kan kasar ta Habasha tana mai cewa lalle kasar na cikin mawuyacin hali, inda kabilun kasar su kimanin 120 ke kara nuna bukatar samun 'yancin cin gashin kan jihohinsu har izuwa 'yancin kai gaba daya. A kullum ana samun rigingimu dangane da mallakar filayen noma. A makotanta kamar su Sudan ta Kudu da Somaliya ana fama da yakin basasa, amma Habasha ta zama kasa mai taka rawar samar da zaman lafiya a yankin yayin da a Kenya da kawo yanzu take taka wannan rawa, ta yi rauni sakamakon rikicin siyasa na cikin gida. Ba wa al'umma cikakken 'yancin ka iya zama mashala ga rikicin na Habasha, inji jaridar.

Joseph Kabila Präsident Demokratische Republik Kongo
Shugaban kasar Kwango, Joseph KabilaHoto: Getty Images/AFP/T. Mianken

Shugaba Joseph Kabila na Kwango na ci gaba da kankane madafun iko inji jaridar Süddeutsche Zeitung a labarin da ta buga dangane da takaddamar da ke kara muni tsakanin Shugaba Kabila da majami'ar Katholika mai babban tasiri a kasar ta Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Jaridar ta ce a ranar 21 ga watan janeru da ya gabata rikicin Kwango ya kai sabon matsayi na muni, inda majami'un kasar suka shiga jerin masu zanga-zangar adawa da Kabila wanda wa'adin mulklinsa ya kare tun a Disamban 2016, amma kuma ya ki gudanar da sabon zabe kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanadar. Yanzu haka dai Kabila da hukumomin gwamnatinsa sun fi iko ne da babban birnin kasar wato Kinshasa yayin wasu sassan kasar ke fita hannunsu. Ga rikice-rikice na kungiyoyi 'yan takife cikinsu ma har da sojojin gwamnati da 'yan sanda da suka kwashe tsawon lokaci ba a biya su albashi ba.

Afrika Kenia Altkleider
Masu saya da sayar da kayan gwanjo a kasuwar Kibera da ke Nairobi.Hoto: AP

Masakun tufafi a Afirka sun ruguje a cewar jaridar Neue Zürcher Zeitung. Ta ce tsoffin tufafi musamman na gwanjo da kuma sabbin da ake sumogarsu daga kasar Sin zuwa Afirka sun taka rawa wajen durkusar da masana'antun tufafi da a baya suka kasance masu tagomashi a nahiyar Afirka. Jaridar ta ce saboda arahar tufafin daga ketare, ya sa wadanda ake samarwa a cikin gida ba sa iya gogayya da su.