1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojan Nigeria 1 ya rasa ransa a yankin Darfur na ƙasar Sudan

May 30, 2006
https://p.dw.com/p/BuwB

Soja 1 na Taraya Nigeria, ya rasa ransa, a yayin da wasu 5 kuma, su ka ji mummunan raunuka, a yankin Darfur na ƙasar Sudan.

Sanarwar, ta hito daga cibiyar ƙungiyar Taraya Afrika, dake Addis Ababa, a ƙasar Ethiopia.

Tun shekara ta 2004 Ƙungiyar Au, ta tura sojojin shiga tsakani dubu 7, a wannan yanki, dake fama da yaƙe yaƙe.

Komishinan tsaro, na Ƙungiyar tarayya Afrika, Said Djinnit, ya bayana matuƙar damuwa, a dangane da wannan ɗanyan aiki.

Ya zuwa yanzu kuma, ba a gano ba, a zahiri mutanen da ke da alahakin kissan.

Komishinan, ya dangata al´amarin da saɓawa yarjejeniyar zaman lahia, da ɓangarori daban daban masu gaba da juna, a Sudan, su ka rattaba hannu kanta, a birnin Abuja ranar 5 ga watan da mu ke ciki.

Wannan Kissa, ya biwo bayan harin da wasu mutane ɗauke da makamai su ka kai, ga sansanin sojojin shiga tsakani na Au, da ke yankin Darfur.

Tun zuwan rundunar tsaron kungiyar taraya a kasar Sudan, wannan shine soja na 6, da ya rasa ran sa.