1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Amurka uku sun mutu a Iraqi

May 5, 2006
https://p.dw.com/p/BuzX

Sojojin Amurka uku sun rugamu gidan gaskiya a Iraqi. Hakan dai ya faru ne bayan da wani bom ya tashi da motar da suke ciki a kudancin birnin Bagadaza a yau juma´ar nan.

Ko da yake rundunar yan sandan yankin ta tabbatar da faruwar wannan al´amari, to amma ya zuwa yanzu taki tace komai dangane da yadda al´amarin ya faru.

Daga dai tun lokacin da sojin na Amurka tare da sojojin kawance suka afkawa kasar ta Iraqi da yaki, ya zuwa yanzu sojojin Amurka kusan dubu biyu ne suka rugamu gidan gaskiya.