1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

SOJIN ITALIA 12 SUN MUTU A IRAKI

ZAINAB AM ABUBAKAR.November 12, 2003
https://p.dw.com/p/Bvnf
Ayau kimanin yansandan Italia 12 suka rigamu gidan gaskiya lokacin da wani bomb ya tarwatse a birnin Nasiriyya dake kudancin kasar Iraki.Rahotanni daga headquatan rundunar na nuni dacewa 9 daga cikinsu yansanda kwantar da tarzoma ne ayayinda sauran biyun sojoji,harin daya kasance na farkon irinsa daya ritsa da dakarun Italiyan a wata kasa.Kakakin rundunar dake Birnin Rome,Alessandro Di Gruttola,ya fadawa manema labaru cewa da dama daga cikinsu sun samu raunuka sakamakon harin.

Kasar ta Italiya nada kimanin dakarunta 2,300 akudancin Iraki,masu yawa daga cikinsu kuwa nada sansanoninsu a Nasiriyya,garin da ake zaman lafiya tunda sojojin taron dangin suka mamaye wannan kasa.

An dai tura dakarun Italiyan ne da nufin taimakawa wajen tsaro,tonon binannun nakiyoyi,tare da taimakawea wajen ginin filayen asibitoci da gyaran bututun samarda ruwa a wannan yankin.

To sai dai acan Itali ayayinda dubban yan jammiyyun adawa ke kira da janye dakarun kasar tare da mayar dasu gida,Prime minister Silvio Berlusconi yace wannan hadari daya ritsa da rayukan dakarun kasar 12 tare da raunana wasu 13,ko kadan bazai barazana su ba.Yace babu wata barazana da zata hana kasar sa taimakawa wajen farfado da Iraki da halin da take ciki.

Yan adawan dai na zargin gwamnatin Italiya da amfani da yan kasar wajen dadada gwamnatin Bush ba tare da laakari da hadarin dake tattare da hakan ba.A dangane da hakane dukkan jammiyun suka hade wajen kira da akomar da dukkas dakarun kasar da aka jibge a Iraki. A hannu guda kuma a daren jiya ne wani sojin Amurka ya bakunci lahira,lokacin da wani bomb ya ritsa dashi a arewacin Iraki.Wannan ya kawo ga adadin dakarun Amurkan 155 suka rasa rayukansu ta wannan hanya a kasar ta Iraki.

Yau ne kuma yansandan kasar ta Iraki da aka bawa horo na musamman kimanin 400,suka fara wani bincike na kutsawa gidajen mutane dake da zama a mahaifar Sadam Hussein dake garin Tikrit.Shugaban yansanda na wannan yankin ya bayyana cewa suna zargin cewa wadanda suka harbo jirgin Amurka ranar jummaa nada zama a wannan gari.

Wannan shine karo na farko da jamian tsaron Iraki suka fara irin wannan bincike kai tsaye ba tare da hadewa da dakarun Amurka ba.