1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Libiya sun kwace birnin Sirte da IS

Gazali Abdou Tasawa
December 5, 2016

Dakaran gwamnatin kasar Libiya sun yi nasarar kwace illahirin birni Sirte daga hannun mayakan kungiyar IS bayan da aka share watannin shida ana gwabzawa tsakanin bangarorin biyu a ciki da kewayen birnin. 

https://p.dw.com/p/2Tn48
Libyen Angriff libyscher Streitkräfte auf IS in Sirte
Hoto: Reuters/G. Tomasevic

Tuni ma dai gwamnatin hadin kan kasar ta bayyana gamsuwarta da maido da wannan birnin wanda ya ke mahaifar tsohon shugaban kasar marigayi Kanal Gaddafi a karkashin ikonta. Kakakin rundunar sojin gwamnatin hadin kan kasar ta Libiya a birnin na Sirte Reda Issa ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa AFP cewa a yanzu sun karya lagon kungiyar ta IS daga cibiyar tata ta birnin Sirte inda da dama daga cikin mayakanta su ka yi saranda tare da mika wuya. 

Sai dai sojojin gwamnati kimanin 700 ake kyautata zaton sun kwanta dama a yayin da wasu dubu uku suka ji rauni a cikin fadan wanda ya bada damar kwato birnin da ya fada a hannun Kungiyar ta IS a watan Yunin shekarar 2015.