1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojin Pakistan sun kai hari sansanin yan Alqaida

January 16, 2007
https://p.dw.com/p/BuUJ

Sojojin Pakistan sun sanar da cewar sun lalata wurare uku da ake zaton maboyar mayakan kungiyar al-Qaeda ne.

An dai sami nasarar hakan ne bayan kai wasu hare-haren bom a kusa da iyakar kasar da Afghanistan, inda har suka kashe mutane da daman gaske.

Wani kakakin rundunar sojan ta Pakistan yace jiragen saman yakin kasar sun kai hare-haren ne a kudancin lardin Waziristan, bayan da aka sami labarin cewar mayakan kungiyar al-Qaeda talatin sun buya a wannan yanki.

Kakakin na soja, Manjo-janar Shaukat Sultan yace wasu daga cikin wadanda aka kashe yan kasashen ketare ne, ko da shike ba’a san yawan su ba.

A watan Satumba na bara, gwamnatin Pakistan ta cimma yarjejeniya da shugabannin kalibun yankunan kasar, a game da farautar yan tarzoma na al-Qaeda a yankunan su.