1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji kussan 30 sun rasa rayuka a cikin harin ƙunar baƙin wake a Kabul

September 29, 2007
https://p.dw.com/p/Bu9w

Kimanin sojoji 30 su ka rasa rayuka, sannan da dama su ka ji raunuka, a cikin wani mummunan harin ƙunar baƙin wake da yan taliban su ka kai sahiyar yau a birnin Kabul na ƙasar Afghanistan.

Ƙungiyar Taliban ta ɗauki alhakin kai wannna hari.

Idan ba manta ba, a farkon watan Ramadan, ta alkawarta matsa ƙaimi wajen kai hare-hare, ga dakarun ƙasa da ƙasa dake Afghanistan.

Wannan shine hari mafi muni da ya rutsa da sojojin ƙasar Afghanistan a fafatawar su da yan Taliban, tun daga kifar da mulkin Mollah Umar a shekara ta 2001.

Shugaban ƙasa Hamid Karzai, ya alkawarta lunka ƙoƙari bisa ƙoƙar,i domin murƙushe mayaƙan Taliban, tare da taimakon dakarun ƙungiyar tsaro ta NATO, saidai har ya zuwa yanzu, haƙar ta kasa cimma ruwa.

A jawabin da ya gabatar gaban Majalisar Ɗinkin Dunia ranar laraba da ta wuce, Karzai ya nunar da cewa, an cimma babba nasara ta fanin samar da kwanciyar hankali a ƙasar, duk da cewar har yanzu akwai sauran rina kaba.