1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojoji sun rushe gidan jagoran 'yan Shi'a a Zaria

Salissou BoukariDecember 13, 2015

Sojoji sun hallaka 'yan Shi'a da dama a birnin Zaria na Tarayyar Najeriya cikin su har da manya-manyan maluman mashabar a wani samame da suka kai gidan jagoran 'yan Shi'an.

https://p.dw.com/p/1HMlL
Hoto: A. Abubakar/AFP/Getty Images

Shaidun gani da ido sun ruwaito cewa jami'an tsaron sun kona gidan jagoran na 'yan Shi'a tare da rushe shi. Sai dai kuma a halin yanzu ba'a san inda shugaban na 'yan Shi'a Cheik Ibrahim El-Zakzaky yake ba. Malam Isa daya daga cikin 'yan Shi'an, a birnin na Zaria, ya shaida wa wakilinmu na Kaduna Ibrahima Yakubu cewa Sojojin sun kashe dumbun mabiya mazahabar ta Shi'a da suka taru a gidan babban malamin na su domin bashi kariya, inda ya kara da cewa, a halin yanzu ba su san yadda sojojin suka yi da gawawakin 'yan uwan na su da aka karkashe ba, sannan kuma ya kara da cewa an rusa masallacin Husainiyya tare kuma da kame wasu mata da dama.

A ranar Asabar ne dai rigima ta barke a tsakanin mabiya mashabar ta Shi'a da wasu Sojojin kasar, inda rundunar Sojan ta Najeriya ta ce 'yan kungiyar sun afka wa tawagar babban hafsan sojojin Kasar da makamai, zargin da 'yan Shi'an suka musanta.