1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Amurika 7 sun mutu a Irak

April 2, 2007
https://p.dw.com/p/BuOO

Duk da matakan tsaron da ƙawancen sojojin Amurika da na Irak, ke ci gaba da ɗauka a Irakin, yan yaƙin sari ka noƙe na ci gabada da kai hare-hare a sassa daban daban na ƙasar.

Kommandan rundunar sojojin Amurika, a birnin Bagadaza ya ce tsakanin asabar da lahadin da su ka wuce, yan ƙunar baƙin wake, sun hallaka ƙarin sojojin 7 na Amurika.

Daga farkon wannan yaƙi a watan Maris na shekara ta 2003,ya zuwa yanzu, a jimilce dakarun Amurika 3.250 su ka sheƙa lahira, a fagen daga.

Itama Britania, babbar abikiyar ƙawacen Amurika ta yi asara sojanta daya a jiya lahadi a birnin Bassorah, wanda shine cikwan sojoji 135 da kasar ta rasa a Iraki.

Britania nanda sojoji fiye da dubu 7 awananyanki, saidai a watan Februaru da ya wuce, Praminsita Tony Blair, bayan matsin lambar da ya fuskanta, a cikin gida ya bayyana aniya fara janyewar sojojin Engla daga Iraki, a yan wattani masu zuwa