1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin gwamnatin Sri Lanka na yiwa yankunan ´yan tawaye ruwan bamabamai

June 16, 2006
https://p.dw.com/p/Butn

Sojojin Sri Lanka sun sake kai farmaki akan garin Kilinochi wanda ya kasance sansanin ´yan tawayen Tamil Tigers dake arewacin kasar. Hakan na matsayin martani ga wani mummunan hari da aka kai kan wata safa a ranar alhamis wanda yayi sanadin mutuwar mutane 64 sannan wasu dama suka jikata. Babban sakataren MDD Kofi Annan yayi kashedi game da rura wutar wani yakin basasa a kasar, sannan a lokaci daya yayi kira ga sassan biyu da su koma ga girmama yarjejeniyar tsagaita bude wuta. To amma a nasa bangaren ministan harkokin wajen Sri Lanka Mangala Samaraweera cewa yayi yanzu hakurinsu ya kai makura, a saboda haka ya zama wajibi gwamnati ta dauki takaitattun matakai na tsoratarwa.