1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Habasha sun kutsa cikin birnin Wajid na Somalia

July 22, 2006
https://p.dw.com/p/Buph
Rahotanni daga Somalia sun ce sojojin Habasha wadanda suka kutsa cikin kasar don ba da kariya ga gwamnatin wucin gadi, bisa ga dukkan alamu sun kutsa cikin wani birni na biyu a Somalia. Mazauna da kuma kungiyoyin ba da agaji sun rawaito cewar a daren jiya sojojin Habasha kimanin 200 sun kutsa cikin birnin Wajid inda suka karbi ikon filin saukar jirgin sama. Da farko dai an ba da rahoton cewa Habasha ta tura sojojinta birnin Baidowa mazaunin gwamnatin wucin gadin Somalia. To amma Habasha da kuma gwamnatin Somalia wadda ke kara fuskantar barazana daga mayakan Islama dake rike da birnin Mogadishu sun musanta rahotannin. Yanzu haka dai kotun kolin shari´ar musulunci ta Somalia ta kaddamar da jihadi akan sojojin kutsen.