1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraki na samun nasara kan IS a Tal Afar

Gazali Abdou Tasawa
August 26, 2017

Dakarun gwamnatin Iraki sun yi nasarar kwace iko da tsakiyar birnin Tal Afar daga hannun mayakan kungiyar IS kwana bakwai bayan kaddamar da harin neman kwace birnin.

https://p.dw.com/p/2itFX
Offensive gegen die IS-Terrormiliz im Irak
Hoto: picture-alliance/dpa/AP/B. Szlank

Dakarun gwamnatin Iraki sun yi nasarar kwace iko da tsakiyar birnin Tal Afar daga hannun mayakan kungiyar IS kwana bakwai bayan kaddamar da harin neman kwace birnin da ke zama daga cikin garuruwan karshe da ke a hannun kungiyar ta IS a Iraki. A wannan Asabar dakarun gwamnatin Irakin sun yi nasarar kwato unguwanni shida. 

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da wata tawagar ministocin harakokin wajen da na tsaron kasar Faransa Faransa Jean Yves Le Drian da Florence Parly ke wata ziyarar aiki a birnin Bagadaza domin jaddada wa mahukuntan kasar ta Iraki goyon bayan Faransa a yakin da suke yi da Kungiyar IS.

Kwace birnin Tal Afar dai zai bai wa sojojin iraki da na rindunar kawancen kasa da kasa damar datse zirga zirgar mayakan IS da ma makamai tsakanin kasashen Iraki da Siriya.