1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Iraqi za su karbi ragamar tsaro a shekara mai zuwa

August 2, 2006
https://p.dw.com/p/Buo6

Shugaban kasar Iraqi jalalal Talabani, yace dakarun sojin kasar za su karbi ragamar gudanarwar tsaro a fadin kasar Iraqi a karshen shekarar badi. Yace sannu a hankali dakarun za su rika karbar ragamar gudanarwa na larduna tare kuma da fatan cewa ya zuwa karshen shekarar za su kawo karshen ayyukan tarzoma a kasar baki daya. Hasashen shugaban na karfin sojin kasar Iraqin ya zo ne mako guda kacal bayan sanarwar Amurka na tura karin sojoji 3,500 zuwa Bagadaza babban birnin kasar domin dawo da doka da oda. Yayin da a baya dakarun sojin Amurkan dana Iraqi ke ta tattauna batun mika ragamar shaánin tsaron lardunan, a waje guda kuma lardin Muthanna dake kudancin kasar na baiyana shakku na yiwuwar mika ragamar tsaron baki daya ga yan kasar Iraqi a karshen shekara mai zuwa.