1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Jamus Zasu Je Kongo

May 17, 2006

Majalisar Ministocin Jamus ta amince da shawarar tura sojojin kasar zuwa Kongo

https://p.dw.com/p/Bu00
Sojan jamus a Kongo
Sojan jamus a KongoHoto: picture-alliance / dpa/dpaweb

Majalisar ministocin ta Jamus ta fito fili tana mai yin na’am da shawarar tura sojojin kasar zuwa Kongo. A karkashin kudurin da majalisar ministocin ta yanke za a shigar da sojojin Jamus 800 a rundunar kiyaye zaman lafiya da Kungiyar Tarayyar turai zata tura zuwa kasar ta Kongo domin sa ido akan zaben da aka shirya gudanarwa karshen watan yuli mai zuwa. A tsakanin wadannan sojoji akwai jami’an jiyya da na sadarwa 280. Ministan tsaro Franz-Josef Jung ya bayyana gamsuwarsa da shawarar da majalisar ministocin ta tsayar, wadda ya ce ta yi daidai da manufar gwamnati. Jung ya kara da cewar:

“ina farin cikin cewar zamu taimaka wajen ba da cikakkiyar kariya ga zaben saboda dukkanmu muna sha’awar ganin kasar Kongo ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a karkashin wani yanayi na mulkin demokradiyya tsantsa. Domin kuwa hakan zai yi tasiri akan sauran sassa na nahiyar Afurka mai makobtaka da nahiyar Turai. A sabili da haka muke sha’awar samun kyakkyawan ci gaba a wannan yanki.”

A ranar 30 ga watan yuli mai zuwa ne aka shirya gudanar da zaben demokradiyya na farko a kasar kongo. Domin tabbatar da cewar zaben ya tafi salin-alin ba tare da hargitsi ba Kungiyar Tarayyar Turai zata tura dakarun soja 1500 domin sa ido akan zaben tun daga ranar gudanar da shi har tsawon watanni hudu. Sojojin Jamus za’a tsugunar dasu ne a fadar mulki ta Kinshasa, kamar yadda ministan tsaro Franz-Josef Jung ya nunar. Amma duk da haka aikin na kiyaye zaman lafiya yana tattare da hadarin gaske, musamman ma ganin yadda ake sabani kansa. ‘Yan adawa da na jam’iyyar Free Democrats sun soki manufar da kakkausan harshe. Wolfgang Gerhardt daga jam’iyyar ta FDP ya ce babu wani takamaiman shirin da aka yi wa wannan mataki:

“Bisa ga dukkan alamu yawan sojojin da za a tura bai taka kara ya karya ba. Kuma zabe na demokradiyya a kasar Kongo ba zai yi wani tasiri ba, sai fa idan an gudanar da shi a dukkan sassa na kasar ne a cikin kwanciyar hankali. Bugu da kari kuma ba wanda zai iya yin hasashen abin da zai biyo baya, idan an janye sojojin bayan watanni hudu kacal. Wannan shi ne abin dake ci mana tuwo a kwarya.”

A yanzun dai ba abin da ya rage illa ita kuma majalisar dokoki ta Bundestag ta albarkaci lamarin, wanda kuma ko shakka babu zata yi hakan da babban rinjaye.