1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Koriya ta kudu sun fara barin Iraqi

May 9, 2006
https://p.dw.com/p/Buz6

ƙasar Koriya ta kudu ta fara janye sojojin ta daga Iraqi a yau Talata. Koriya ta kudu na da dakaru 3,600 a ƙasar Iraqi wadanda suke jibge a arewacin lardin Arbil inda suke aikin kiyaye zaman lafiya da kuma taimakawa aikin sake gina ƙasar. A shekarar da ta gabata majalisar dokokin ƙasar ta amince da rage dakaru 1000 bayan yabawa da rawar gani da sojojin suka taka. ƙasashen Amurka da Britaniya su ne ke da dakaru mafi yawa a Iraqi. Shi ma sabon P/M Italiya mai jiran gado Romano Prodi ya baiyana aniyar janye sojojin Italiyan su 3,000 dake cikin dakarun ƙawance a Iraqi bayan tattaunawa da Amurka da kuma hukumomin Iraqi.