1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sojojin Sudan sun kara da yan tawaye a Chadi

October 8, 2006
https://p.dw.com/p/Bugu

Rahotanni daga Sudan sunce sojojin kasa sun ratsa gabashin Chadi inda suka fafata da yan tawayen Darfur.

Fadan tsakanin sojin na Sudan da yan tawayen kungiyar JEM ya faru ne a garin Bahai,mai kilomita 900 daga birnin D’jemmena.

Wani maaikacin agaji da yaki a baiyana sunansa ya fadawa kanfanin dillancin labaru na AFP cewa an kwashe wadanda suka samu rauni su kusan 317 zuwa asibiti.

Kakakin gwamnati Hourmadji Moussa yace bai san komai ba game da wannan fada.

A watan agusta ne dai,Chadi da Sudan suka sake bude bakin iyakokinsu,tare da komawa huldar diplomasiya da suka katse a watan afrilu.

Chadin ta zargi sudan da taimakawa yan tawayen gabashin kasar Chadin.

Sudan a nata bangare kuma ta zargi Chadi da baiwa yan tawayen Darfur matsuguni.