1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke izinin zama ɗan ƙasar Jamus ga wani ɗan usulin Nigeria

May 24, 2006
https://p.dw.com/p/Buwy

Kotun Koli ta nan Jamus ta zartar da hukunci cewa ana iya soke izinin ɗan ƙasa ga baƙi yan ƙasashen waje waɗanda aka ba su fasfo ɗin ƙasar Jamus idan aka gano cewa sun bada bayanan karya domin cika sharuɗan da ake buƙata a gare su. Kotun ta fayyace cewa waɗanda suka bada bayanan ƙarya basu da wani hurumi na kariya a ƙarkashin kundin tsarin mulkin Jamus duk kuwa da cewa tsarin mulkin ya yi hani ga karɓe yancin ɗan ƙasa. A ƙarkashin wannan hukuncin kotun tsarin mulkin ta Karlsruhe ta yi watsi da ƙarar da wani ɗan Nigeria dake da fasfo din Jamus ya gabatar na ƙalubalantar janye izinin ɗan ƙasa da aka bashi, bayan da hukumar jihar Baden Wurttemberg dake kudancin Jamus ta gano cewa ya yi ƙarya a bayanan da ya bayar wajen cike takardun neman izinin zama ɗan ƙasar Jamus.