1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somalia ta rufe wani yanki na kan iyakarta da Ethiopia

October 7, 2006
https://p.dw.com/p/Buh2

Hadaddiyar kungiyar kotunan Islama a Somalia ta ba da umarnin rufe wani sashe na kan iyakarta da makwabciyarta Ehiopia, inda ta zargi dakarun Ethiopia da yi mata kutse da binne nakiyoyin karkashin kasa da kuma kai farmaki a yankin kasar ta Somalia. A daidai lokacin da ake fargabar barkewar wani rikici tsakanin kasahen biyu, kotunan Islama a Somalia sun rufe kan iyakar dake yankin Hiran bisa dalilai na tsaro. A kuma halin da ake ciki dubban ´yan kasar ta Somalia na kwarara cikin Kenya, don kauracewa sojoji sa kai na Islama. A dangane da haka yanzu sansanin ´yan gudun hijira a Kenya ya cika da masu neman mafaka, inji mai magana da yawon hukumar da ´yan gudun hijira ta MDD Jennifer Pagonis.

“A kullum mutane kimanin dubu 1 ke shiga cikin Kenya, ya sa mun kai makura ga irin taimako musamman na samar musu da muhalli a sansanonin ´yan gudun hijira guda 3 da muke da su a yankin Dadaab.”