1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somalia ta zargi abokan gaba da kokarin ta da zaune tsaye a cikin kasar

June 24, 2006
https://p.dw.com/p/Busf

Sojojin sa kai na Islama da suka kwace iko a babban birnin Somalia sun ce wata abokiyar gaba ta ketare wadda ke son ganin kasar ta sake tsunduma cikin hargitsi bayan an shafe ´yan makwanni kalilan ana zaman lafiya, ta shirya kisan da aka yiwa wani dan jaridar Sweden. A gun wani taron gangami da aka yi jiya a birnin Mogadishu aka harbe Martin Adler mai shekaru 47 har lahira. A yau asabar wani jirgin saman kungiyar ba da agaji ta Red Cross ya yi jigilar gawarsa zuwa Nairobi babban birnin kasar Kenya kafin a karasa da ita zuwa Sweden. Shugaban kungiyar kotunan Islama, Sheikh Sharif Sheikh ya ce an shirya kisan ne daga wajen kasar da nufin ta da zaune tsaye a Somalia. To sai dai bai yi karin bayani ba.