1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Somaliya: Amirka ta fatattaki 'yan Al-Shabbab

Salissou Boukari
September 13, 2017

Jiragen yakin Amirka sun kai hare-hare kan 'yan jihadi na Al-Shabbab a kasar Somaliya, inda suka kashe shida daga cikin su. A cewar rundinar kasar ta Amirka mai kula da harkokin Afirka ta AFRICOM.

https://p.dw.com/p/2juoY
General Thomas D. Waldhauser
Hoto: Getty Images/J. Ernst

Rundinar ta AFRICOM ta dauki wannan mataki ne tare da hadin gwiwar gwamnatin kasar ta Somaliya a wani yanki da ke a nisan km akalla 260 a Kudancin birnin Mogadiscio inda aka gano maboyar mayakan. Cikin sanarwa da ta fitar a yau Laraba, Rundunar ta Amirka a Afrika ta ce sojojin Amirka za su dauki dukannin matakan da suka dace domin yakar 'yan ta'adda a duk inda suke a Afrika da ma  duniya baki daya. A watan Maris ne dai da ya gabata, Shugaban Amirka Donald Trump ya bai wa ma'aikatar tsaron kasar ta Pentagone damar yakar 'yan jihadin na Somaliya a wani mataki na goyon baya ga gwamnatin kasar, inda ake fuskantar matsala ta 'yan Al-Shabbab tun daga shekara ta 2007.