1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain ta cafke masu safarar matasa

Yusuf Bala Nayaya
January 4, 2017

Wasu mata uku 'yan asalin kasar ta Najeriya ke tsara jigilarsu zuwa kasar Spain ta jirgin sama bayan sun yi masu takardun bogi.

https://p.dw.com/p/2VFid
Libyen Flüchtlinge nach Rettung durch Küstenwache
Hoto: picture-alliance/dpa

'Yan sandar kasar Spain sun sanar da yin nasarar karya lagon gungun masu safarar bakin haure 'yan asalin Najeriya ta tekun Bahar Rum zuwa Turai

Hukumar 'yan sandar kasar ta Spain ta bayyana wannan nasara da ta samu a cikin wata sanarwa da ta fitar a wannan Laraba inda ta ce masu safarar bakin hauren na yaudarar akasarin mutanen da ba su da galihu a Najeriyar matasa inda a sace suke bi da su ta kasashen Nijar daga nan su ketara zuwa Libiya, kana su yi amfani da wasu mutanen wajen kwasar matasan a cikin jiragen ruwa marasa inganci inda su ke keta tekun Bahar Rum zuwa kasar Italiya.

Mata uku 'yan asalin kasar ta Najeriya ke tsara jigilar zuwa kasar Spain ta jirgin sama bayan sun yi masu takardun bogi ta hanyar amfani da wasu takardun wasu 'yan Najeriya da ke da takardun iznin zaman kasar ta Spain, tare kuma da tilasta masu sanya hannu kan wata takardar bashi na kudi kimanin Euro dubu 40 da za su biya daga baya.