1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Spain ta kori bakin haure ´yan Afirka sama da 700

May 21, 2007
https://p.dw.com/p/BuL4
A cikin makon da ya gabata Spain ta kori wasu bakin haure ´yan Afirka su kimanin 750 wadanda ba su da isassun takardun izinin zama cikin kasar. Bakin dai ba su dade ba da isa tsibiran Canary. A karshen makon jiya aka koma da kimanin 600 daga cikin su ta sama zuwa Senegal. Sannan sauran kuma aka yi jigilar su zuwa kasashen Marokko, Mauritania da kuma Gini-Bissau. Ministan cikin gida Alfredo Perez Rubalcaba ya ce Spain na son ta aike da bayyanannen sako ga mutanen da ke sumogar bakin haure. Jami´ai sun nunar da cewa sama da bakin haure dubu 30 suka shiga tsibiran na Canary a bara kadai.